Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Mutan Gombe Sun Bi Sawun Buhari da Jonathan


Yayinda ranakun zabe ke ta karatowa a Najeriya, a gefe daya jam’iyyun siyasa a Jihar Gombe, sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin zabe da kuma bayansa.

Wannan yarjejeniya a kulla ta ne a gaban kungiyoyin addini, dana hukumar zabe, da kuma hukumar ‘yan sanda, da sauran makamantansu a matsayinsu na shaidu.

Kassim Gaidam, shine Kwamishin zabe a Jihar Gombe.

“Wannan mu muka shirya taro, amma wato kungiyoyin NAREC, wato hadakar kungiyoyin addinai sune suka shirya yarjejeniyar kuma ‘yan sayasan sun yarda sun sa hannu. Kumar yarda da sukayi suka saka hannu, wato kamar sun bi mataki da aka dauka a tarayya”.

Evangelist Musa ne shugaban Matasan Kiristoci na arewa maso gabashin Najeriya.

“Da farko, Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya sa hannu akan wannan yarjejeniya, kuma ya tabbatar da cewa za’a yi zabe cikin lumana da gaskiya da adalci.”

Saleh Sha’aibu shine darekta na tarbiyya na Majalisar Kungiyoyin Matasa Musulmi ta Najeriya.

“Yanzu mu manufarmu shine samar da hanyoyi na daban na ilimantar da mutane.”

Rigigimu masu nasaba da siyasa na daga cikin manyan batutuwan dake ciwa jama’a tuwo a kwarya musamman ma ganin babban zaben Najeriya na karatowa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG