Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Suka Yiwa 'Yar Shekara 11 Fyade a Garin Salkan Jihar Neja


Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello

Dr. Haruna Musa Bahago da wasu mutane goma sha biyu suka yiwa 'yarsa mai shekaru goma sha daya fyade a garin Salka ya rubuta wasikar koke bisa ga irin hukumcin da kotun magistrate ta yanke da yadda aka yi masa kan diyarsa .

Tun ranar 19 na watan Disambar bara ne lamarin ya faru kuma yanzu haka yarinyar tana dauke da ciki.

An kama mutanen goma sha biyu da suka aikata aika aikar tun a lokacin kuma sun amfa laifinsu. To saidai kotun magistrate dake garin Nasko ta ci mutanen tarar Naira dubu dari biyar da ishirin (N520,000). Amma kafin shari'ar sai da 'yansandan Nasko suka karbi N325,000 daga hannun mutanen.

A wasikar koken da Dr Haruna Bahago mahaifin yarinyar ya rubuta yace cikin tarar da kotun ta ci mutanen N28,000 aka bashi domin wai, ya je ya kula da diyarsa wadda yanzu take da juna biyu. Dalili ke nan da Dr. Bahago ya rubuta wasikar kokensa ga kwamishanan 'yansandan jihar.

Barrister Ibrahim Rege shi ne lauyan Dr. Haruna Bahago. Ya lissafa laifin mutanen. Na daya fyade laifi ne. Cikin maza 12 da suka yi ma yarinyar fyade karaminsu shi ne mai shekaru 24 kuma dukansu sun amsa laifinsu gaban kotu. Na uku ita kotun N28,000 kacal ta ba Dr Bahago ya je ya kula da diyarsa. Na hudu yarinyar tana gida babu lafiya. Abun da 'yansanda suka karba da tarar da kotu ta ci mutanen N845,000 ne.

Dr. Bahago ya bukaci kwamishanan 'yansandan jihar ya sake kama mutanen a yi masu shari'a ta zahiri.

Ma'aikatar shari'ar jihar tace ta san da batun kuma tana bincike domin gano gaskiyar maganar. Shi ma kakakin 'yansandan jihar DSP Bala Elkana ya tabbatar da cewa kwamishanan ya samu wasikar koken kuma ya bada izinin a yi bincike.

Ita ma ma'aikatar kula da hakkin yara ta sanar da shiga lamarin.Barrister Maryam Kolo ita ce babbar daraktar ma'aikatar tace mahaifin yarinyar yayi alkawarin kawo masu ita.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG