Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 14 sun Mutu Sanadiyar Hadarin Mota a kan Hanyar Bauchi


Wasu motoci biyu dauke da mutane a ciki, kirar bos mallakar kamfanin Safara na jihar Gombe, sun kara kuma mutane goma sha hudu sun mutu.

Wani hadarin mota na taho-mu-gama yayi sanadiyar kashe mutane goma sha hudu a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe a yammacin jiya Alhamis a garin Alkaleri dake jihar Buachi.

Wani ganau ya fadi cewa wasu motoci biyu dauke da mutane a ciki, kirar bos mallakar kamfanin Safara na jihar Gombe, wato Gombe Line, sun kara a kan hanyarsu ta zuwa Birnin tarayya Abuja domin halarta wani taron kara ma juna sani a fannin harkar noma. ya kara da cewa akwai wani mai babur da hadarin ya rutsa da shi.

Hadarin dai ya shafi motar ‘yan jaridar gidan gwamnatin jihar Gombe akan hanyarsu ta komawa gida bayan kammala taron yakin neman zabe na jam’iyyar PDP wanda shugaba Jonathan yayi a garin Bauchi. Mutane da yawa sun sami raunuka sandiyar hadarin inji Usman Mu’azu. Sai dai dogarin gwamnan jihar Ibrahim Isah, ya tabbatar da cewa Gwamnan baya cikin tawagar a lokacin da hadarin ya faru.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG