Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 150 Suka Mutu Sakamakon Hadarin Da Wata Tankar Mai Tayi A kasar Pakistan


Explosion in Podgorica

A Pakistan, jami'an kasar sunce wata tankar mai data yi hatsari, ta yi binidga ta kama da wuta, ta kashe akalla mutane 150

Maza da mata da yara,wadanda suka suka garzya inda ta kifen domin kwasar ganima. Hukumomin kasar suka ce fiye da mutane 100 ne suka jikkata a fashewar, kuma da yawa daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
Tankar tana taso ne daga birnin karachi mai tashar jiragen ruwa dake kudancin kasar, zuwa Lahore hedkwatar lardin Punjab, sa'ilinda motar ta kubucewa matukinta. Sanarwar da aka bayar ta na'urori masu kara sauti a wani masallaci cewa wata tankar mai tayi hadari har mai yana yoyo, yasa mnazauna kauyuka da suke kusa suka dunguma zuwa wurin domin kwasar mai. A lokacin ne kuma motar tayi bindiga ta apka kan wadanda suke wurin da kuma motoci da suke kusa.
Man fetur abune da yake da tasiri a Pakistan, duk d a hadari dake tattare da shi, tunanin samunsa kyauta yana sa mutane su mance da hadarin dake tattare da kwasar ganima.
Babu tabbas kan abunda yasa tankar tayi bindiga. Amma Yansanda dake yankin sun ce matukin ya tsira da ransa kuma tuni aka kama shi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG