Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 74 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Wasu Hare-Hare A Jihar Benue


Gwamnan Benue Samuel Ortom
Gwamnan Benue Samuel Ortom

An kashe akalla mutane 74 a jihar Benue da ke Najeriya a wasu hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a karshen mako, a cewar jami’an yankin da ‘yan sanda ranar Asabar. Wannan shi ne rikici na baya-baya a yankin da ke fama da tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma.

Tashin hankali ya karu a cikin 'yan shekarun baya-baya a jihar Benue yayin da karuwar yawan jama'a ke haddasa fadada filayen noma, lamarin da ya sa babu filayen kiwo sosai don makiyaya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue Catherine Anene, ta ce an gano gawarwaki 28 a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mgban tsakanin yammacin ranar Juma’a zuwa safiyar Asabar.

'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.
'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Nan take dai ba a san dalilin harin ba amma wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigar sun je wurin ne suka fara harbe-harbe tare da kashe mutane da yawa.

Wannan na zuwa ne bayan wani lamari na dabam da ya faru a jihar a ranar Laraba a kauyen Umogidi da ke karamar hukumar Otukpo, lokacin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe mazauna kauyen a wurin wani taron jana’iza, abinda Bako Eje, shugaban karamar Otukpo, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters kenan.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

A wata sanarwa da aka fidda ranar Asabar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen gomman mutane da aka yi a jihar Benue a kwanan nan a yankin Umogidi, ya kuma umurci jami’an tsaro su kara sa ido a yankunan da lamarin ya shafa.

XS
SM
MD
LG