Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 80 Suka Mutu A Yunkurin Ceto Ma'aikatan Kamfanin Gas na Algeriya


Kamfanin gas na Algeriya
Kamfanin gas na Algeriya
Jami’an kasar Algeria sun ce garkuwa da ma’aikata da mayakan kishin Islama suka yi da kuma sumamen sojan da aka kai a masana’antar iskar gas dake Hamada sun yi sanadin mutuwar mutane 80, da suka hada da ‘yan kasashen ketare da dama.

Jami’ai da suke binciken ginin sun gano wadansu karin gawarwaki 25 jiya Lahadi, sai dai sun ce jikunansu sun yi kaca kaca, yana da wuya a tantance ko mayaka ne ko kuma wadanda aka yi garkuwa da su ne.

Mayakan kasar Algeriya sun kama mayaka biyar da rai lokacin da suka kai sumamen.

Kamfanin dillancin labaran kasar Algeria yace mayakan sun kashe mutane bakwai daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su lokacin da aka kai sumamen, yayinda dakarun Algeriya suka kashe mayakan da suka yi garkuwa da su 11. An kuma kashe mayaka da wadanda aka yi garkuwa da su da dama tun farkon gumurzun, yayinda wadansu mutanen da aka yi garkuwa da su suka tsira da ransu.

Mayaka sun kwace masana’antar iskar gas ta Ain-Amena ranar Laraba.
Shugaban kungiyar mayakan kishin Islama Mokhtar Belmokhtar ya dauki alhakin kai harin. A cikin hoton bidiyo da ya buga a shafin internet jiya Lahadi, yace ya dauki wannan matakin ne da yawun kungiyar al-Qaida ya kuma bayyana cewa mayaka 40 ne daga kasashen Musulmi da na yammaci suka kai harin.
Belmokhtar yace harin martani ne kan matakin sojan da Faransa ta ke dauka a kan mayakan dake da alaka da kungiyar al-Qaida a Mali.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG