Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 85 Suka Raunata Sanadiyar Faduwar Wani Jirgin Saman Mexico


'Yan kwanakwana da masu aikin ceto a wurin da jirgin saman ya fadi
'Yan kwanakwana da masu aikin ceto a wurin da jirgin saman ya fadi

Wani jirgin sama mallakar kamfanin Aeromexico ya fadi cikin kasar Mexico a jihar Durango a arewacin kasar kuma ya yi sanadiyar jikata mutane 85

Mutum tamanin-da-biyar sun samu raunuka, bayan da wani jirgin saman fasinja mallakar kamfanin Aeromexico ya fadi a jihar Durango da ke arewacin kasar, amma dai babu wanda ya mutu, kamar yadda gwamna Jose Rosas Aispuro Torres ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Jirgin mai lamba biyu-hudu-uku-daya, ya fadi ne, mintina kadan bayan da ya tashi daga filin jirage na Durango Guadalupe Victoria a jiya Talata, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Mexico.

Gwamna Torres ya fadawa manema labarai cewa, matukin jirgin ya yi kokarin ya katse tafiyar bayan da ya fahimci cewa yanayi ba shi da kyau, amma kuma ya makara.

Rahotanni kan yanayi, sun nuna yadda hadari ya bazu a yankin a lokacin da hadarin ya auku.

Fasinjoji 97 da ma’aikata hudu ne a cikin jirgin mai kirar Embraer 190.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG