Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 9 Suka Mutu Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Tekun Bahar Rum - Jami'an Tsaron Gabar Tekun Italiya


Hadarin kwale-kwale
Hadarin kwale-kwale

Mutane 9 da suka hada da jariri daya ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwalen da suke cikin a lokacin da suke kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum a cikin yanayi mai hadari, kuma ana fargabar bacewar wasu mtuane 15, kamar yadda ma’aikatan tsaron gabar ruwan Italiya suka sanar a yau Alhamis.

WASHINGTON, D. C. - Jami’an tsaron gabar tekun Italiya sun ce sun samu bukatar hadin gwiwa daga hukumar bincike da ceto ta Maltese (SAR) bayan da kwale-kwalen ya kife a nisan kilomita 50 kudu maso gabashin tsibirin Lampedusa a ranar Laraba.

Jami’an tsaron gabar tekun sun ce sun aike da nasu kwale-kwlaen sintiri zuwa wurin da lamarin ya faru, wanda suka ceto mutane 22 da suka tsira tare da gawarwaki 9 da suka hada da wani jariri.

Ayyukan ceto na fuskantar kalubale musamman saboda rashin kyawun yanayi da yanayin teku a yankin da igiyar ruwa ta kai mita 2.50, in ji masu gadin gabar tekun.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG