Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Ashirin Sun Mutu A Zanga Zangar Kasar Venezuela


Ana fama da karancin kayayyakin masarufi da magunguna a Caracas

A kasar Venezuela kuma yawan mutanen da suka mutu cikin makoni uku da aka yi ana yin zanga zanga da tarzoma ya karu zuwa ashirin a yayinda mutane goma sha daya suka mutu a ranar Alhamis da dare.

Jami’ai sun baiyana cewa a unguwar El Valle ta birnin Caracas ne mutanen suka mutu. Karfin wutar lantarki ta kashe su sa’ilin da suke kokarin satan friji daga wani gidan gasa biredi.

Kusan kullum ake yin mumunar zanga zanga a unguwanin birnin Caracas, a yayinda kasar ke kara tsunduma cikin rikicin tattalin arziki. Yanzu haka ana karancin kayayyakin masarufi, ciki harda kayayyakin abinci da magunguna

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG