Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Ashirin Sun Mutu Sanadiyar Tuntsirewar Jirgin Ruwa


Kimanin mutane tara ne ba’a gansu ba yayinda aka tserar da 30 bayan da wan jirgin ruwa ya tuntsire

Jami’ai a Yammacin Myanmar sun ce wani jirign ruwa dauke da baki da suke hanyar su ta dawowa daga bikin aure ya tuntsire a Kogin Ngawun, in da yayi sanadiyyar mutuwar Mutane 20.

Ma’aikatan ceton gaggawa sunce jirgin ruwan yayi karo ne da wani kwale kwale.

Kimanin mutane tara ne ba’a gansu ba yayinda aka tserar da 30 a cewar jami’ai

Bakin masu biki suna hanyar su ne ta dawowa daga biki a Pathein. Wani Dan sanda yace “akasarin su yan uwane daga kauye guda.”

An saba ganin munanan hadarin jiragen ruwa a Myanmar, wacce aka fi sani da Burma, inda mafi yawan mutane ke tafiya tafiyen su ta hanyar jiragen ruwa inda kulawar gwamnatin tayi karanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG