Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Dake Yankin Catalonia Na Kasar Spain Sunyi Zanga-zangar Lumana


Spain - FILE PHOTO: Catalan pro-independence supporters hold a giant "estelada" during a demonstration in Barcelona

Mazauna yankin Catonia su gudanar da zanga-zangar lumana na ci gaba nuna kokari su na ballewa daga kasar Spain.Jam'a da dama ne suka fito wannan zanga-zangar wanda aka yi cikin kwanciyar hankali

Mazauna yankin Catalonia dake yin adawa da kokarin gwamnatin yankin na ballewa daga kasar Spain, sun yi gangami jiya lahadi a birnin Barcelona.

‘Yan sanda suka ce mutane dubu 350 suka halarci wannan gangami, yayin da wadanda suka shirya shi suka ce mutane har dubu 900 ne suka je. An yi wannan maci cikin lumana, kuma ba a samu wani rahoton tashin hankali ba.

Daya daga cikin ‘yan zanga zangar ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa “sun jima suna yin shiru a kan wannan batu.”

A makon jiya, ‘yan yankin Catalonia sun jefa kuri’ar ballewa daga kasar Spain da gagarumin rinjaye. A wannan kuri’ar raba gardamar da gwamnatin Spain ta ce haramtacciya ce, kashi 90 cikin 100 na mutanen yankin sun amince da yankin ya balle, sai dai kasa da kashi hamsin cikin 100 na masu jefa kuri’a ne suka fita a lokacin zaben.

Kuri’unb neman ra’ayoyin jama’a sun sha nuna cewa mafi yawan mutanen yankin Catalonia sun fi son su ci gaba da kasancewa cikin kasar Spain maimakon su balle su kafa kasarsu.

Facebook Forum

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG