Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 50 Sun Mutu, 200 Sun Ji Rauni A Harin Dan Bindiga A Las Vegas


'Yan sanda a Las Vegas dake Jihar Nevada a Amurka, sun ce wani mutum ya bude wuta a kan masu halartar wasan mawaka na kaboyi cikin daren lahadi, ya kashe mutane akalla 50, tare da raunata wasu fiye da 200, a wannan harin bindiga da ya zamo mafi muni a tarihin Amurka.

Baturen 'yan sandan birnin Las Vegas, Joseph Lombardo, ya shaidawa 'yan jarida cewa maharin ya bude wuta daga cikin wani daki ne a hawa na 32 na wani hotel maio suna Mandalay Bay Casino, wanda ke tsallaken hanya daga filin da ake gudanar da wannan wasa. Hotunan bidiyo sun nuna wadanda suka je kallon wasan suna rugawa da gudu, wasu na neman wurin buya, wasu kuma na ihu a yayin da aka yi ta jin karar bindiga.

Lombardo yace 'yan sanda sun rutsa dan bindigar, kuma ya mutu, yayin da aka samu bindigogi da dama a dakinsa a hotel din. Yace dan bindigar wani dattijo ne mai suna Stephen Paddock, mai shekaru 64 da haihuwa. Yace ana kan binciken Paddock, amma 'yan sanda sun yi imanin cewa shi kadai ne ya kai harin.

Yace ba su san dalilin Paddock na bude wutar ba.

Hukumomin sun kuma yi farautar wata mace da aka ce suna tare da Paddock domin nerman karin bayani. Jami'in 'yan sandan yace an same ta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG