Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 134,000 Ne Ke Dauke Da Coronavirus a Duniya


Kiyasi ya nuna cewa sama da mutum dubu 134 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasashe 114 a duniya, wanda hakan kankanin adadi ne idan aka kwatanta da yawan mutum biliyan bakwai da duniya ke da shi.

Sai dai duk da irin matakan da kasashen duniya suke dauka na dakile yaduwar cutar, wacce ake wa lakabi da COVID-19, cutar ta zama babbar annoba ga duniya.

Kwararru a fannin lafiya a nan Amurka sun ce bullar cutar da aka gani a kasar somin-tabi ne, lamarin da ya sa ake ganin asibitoci za su fuskanci tururuwar wadanda cutar ta harba.

Dr. Robert Wyllie na asibitin birnin Cleveland da ke nan Amurka, ya ce yanzu haka sun mayar da hankalinsu ne kan horar da ma’aikatan kiwon lafiya kan yadda za su tunkari masu fama da cutar.

Ya ce, “Muna horar da ma’aikatan lafiya, kama daga abin da ya hada da yadda za su sanya rigunan kariya da kuma yadda za su kwabe su, domin kada su kansu su kamu da cutar.”

Da dai yammacin jiya Alhamis, hukumomin kasar Canada, suka bayyana cewa, urwagidan Firai Ministan kasar Justine Trudeau ta kamu da cutar, bayan da ta dawo daga wata ziyarar da ta kai birnin London.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG