Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 157 Suka Mutu A Hadarin Jirgin Saman Habasha


Yanzu haka 'yan kasashe 35 hadarin jirgin saman Habasha ya rutsa da su, inda fasinjoji 157 suka rasa rayukansu.

Wani jirgin saman Habasha da ya taso daga Addis Ababa ya yi hatsari jim kadan bayan ya tashi da sanyi safiyar jiya Lahadi.

Babu ko daya daga cikin dukkan fasinjojin 157 da ya tsira da ransa.

Gidan talbijin din yada labaran kasar ta Habasha, ya ce jirgin ya fadi ne a kusa da birnin da ake kira Bishoftu kuma yana dauke ne da fasinjoji daga kasashe akalla 35.

Daga cikin fasinjojin, akwai ‘yan kasar Kenya 32, ‘yan Canada 18, ‘yan Habasha 9 da kuma Amurkawa 8.

Har ila yau akwai ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da dama da suke cikin wadanda suka rasun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG