Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 29 Sun Mutu a Harin Da Aka Kai Gidan Yarin Afghanistan


Wani jami'in tsaro
Wani jami'in tsaro

Akalla mutum 29 ne suka mutu yayin fadan da ake gwabzawa bayan wani mummunan harin da aka kai a wani gidan yari a Afghanistan.

An fara rikicin ne tun daga yammacin ranar Lahadi a garin Jalalabad da ke gabashin Afghanistan.

Aƙalla mutum 29, ciki har da fursunoni, sun mutu, yayin da kusan 50 suka jikkata, a cewar Ataullah Khogyani, kakaki agwamnatin Lardin Nangarhar.

Wata kungiya mai ikrarin jihadi mai suna ISIL ce ta dauki alhakin harin ta kafar kamfannin dillancin labaranta, harin da ya fara da tayar da bam sannan ya biyo baya da ‘yan bindiga da suka kutsa kai cikin gidan yarin.

Wani wanda ya samu raunuka yayin harin
Wani wanda ya samu raunuka yayin harin

Khogyani ya ce jami'an tsaro sun yi nasarar sake kama fursunoni akalla 1000 yayin da suke kokarin tserewa amma bai ce ko akwai wadanda suka tsere a cikin fursunonin ba.

Ya kuma tabbatar da cewa aƙalla maharan uku sun mutu amma wasu da yawa suna makale a cikin gidan yarin ko kuma a gine-ginen da ke kusa, inda suke ci gaba da kai wa jami'an tsaro hari.

A cewar jami'an lardin, sama da fursunoni 2,000 ne a cikin gidan yarin a lokacin da aka kai wannan hari.

Wani ganau mai suna Sohrab Qaderi ya sheda wa kamfanin dillancin labarai cewa an saka dokar zama a gida a Jalalabad yayin faruwar lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG