Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar Na Iya Yiwa Wasu 'Yan Jarida Uku daga Turkiya Hukuncin Daurin Shekara Uku


'Yan jaridan da aka zarga da shiga kasar Myanmar da karamin jirgi mai sarafa kansa da kansa

'Yan jarida uku daga kasar Turkiya sun sabawa dokar kasar Myanmar saboda sun shiga da karamin jirgi mai sarafa kansa da kansa ko Drone ba bisa ka'ida ba, lamarin da ka iya sa a mahukuntasu tare da dauresu har tsawon shekara uku a gidan kaso

Mai yiwuwa, wasu ‘yan jarida uku da direbensu su fuskanci hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekaru uku-uku, bayan da aka zargesu da laifin keta dokar shige da ficen kayayyaki a Myanmar, saboda sun shiga kasar da dan karamin jirgi mara matuki - ko kuma Drone, da nufin yin aiki da shi wajen tsara wani shiri na musamman da gidan talbijin din kasar Turkiyya na TRT ya aika su su yi.

An kama Mok Choy Lin dan kasar Malaysia, da Lau Hon Meng dan kasar Singapore da kuma wani dan jaridar kasar ta Myanmar Ko Aung Naing Soe da direbansu U Hla Tin a Naypyidaw, babban Birnin kasar a ranar 26 ga watan Oktoba, bayan da suka kammala wata hira da wani dan majalisar dokoki, inda daga baya suka yi amfani da jirgin mara matuki domin su dauki bidiyon ginin majalisar ta sama.

Tuni dai har an yanke musu hukuncin daurin zaman gidan yari na tsawon watanni bi-biyu, a matakin hukunci na farko, saboda karya dokar da ke sa ido kan amfani da jiragen sama, wacce aka samar da ita a shekarar alif-dari-tara-da-talatin-da-uku.

Shi dai gidan talbijin din Turkiyya na TRT, ya ce ma’aikatan nasa sun nemi iznin gudanar da wannan aiki, amma jami’in tsaron da ya kama su ya ce ba su bayyana cewa suna dauke da jirgin mara matuki ba, a lokacin da suka shiga kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG