Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nadin Robert Mueller Wani Bita Da Kullin Siyasa Ne - A Cewar Shugaba Trump


Shugaba Trump ya koka akan cewa ba wanda aka taba nadawa ya bincike Hillary Clinton da tsahon shugaba Barack Obama.

A yau Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki nadin mai bincike na musamman da aka yi don ya binciki ko akwai wata alaka tsakani wadanda suka yi masa campaign da Rasha a zaben da aka yi cikin shekarar da ta gabata, yana kiran matakin na “bita da kullin siyasa na tarihi da aka taba gani a Amurka.

A wasu sakonni da ya rubuta a shafinsa na twitter da safiyar yau, Trump yayi korafin cewa ba a taba cewa za a nada wani mai bincike na musamman don ya binciki “duk miyagun abubuwan da aka tabka a lokacin yakin neman zaben abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat ba, wato tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da kuma gwamnatin shugaba Obama da ta shude.

Trump na maida murtani ne akan nadin Robert Mueller, tsohon shugaban hukumar binciken tarayyar da akayi jiya Laraba, don yayi bincike akan yiwuwar wata alaka tsakanin makarabbansa da jami’an Rasha a zaben, don ba Trump damar samun nasara.

Mr. Mueller ya riga ya fara aikin sa, yayinda hukumar binciken FBI da kwamitin binciken bayanan sirri a majalissar dokoki da ta wakilai sun riga sun fara nasu binciken akan yiwuwar katsalandan Rasha a zaben.

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG