Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAFDAC: Ta Shirya Taron Bita Akan Abincin Jarirai


Iyaye mata da jarirai sun jiran karbar allurar rigakafi

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ko NAFDAC a takaice ta shirya wani taron bita wa jami'anta.

Taron an shiryashi ne akan abincin jarirai da nufin horas da jami'an hukumar yadda zasu bi kasuwanni domin hana kasa madarar yara tamkar tumatur ko tattasai. Manufar ita ce a hana sayar da abincin jarirai barkatai ba kan ka'ida ba.

Dadi Nantim Mulak babban jami'in NAFDAC a jihar Neja yace suna son su dinga kula da mutanen dake sayar da madarar yara a kasuwanni saboda gwamnati tana da ka'idar da za'a kiyaye wurin sayar da madarar yara.

Ba'a so a tilastawa mata su sayi madarar shanu suna ba jarirai sai dai idan akwai damuwa da nonon uwar ko kuma babu ita saboda rasuwa ko wani mugun rashin lafiya. Horon saboda a fadakar da ma'aikatan ne.

Da ma hukumomin kiwon lafiya sun dukufa wajen bayyanawa mata mahimmancin shayar da jarirai nonon uwa.

Wajibi ne idan uwa nada rai kuma tana cikin koshin lafiya ta shayar da jaririnta da nononta har na tsawon watanni shida akalla. Nonon uwa ya fi ma jariri anfani. Jariri zai samu kariya mafi inganci a jikinsa tare da kyakyawar kwakwalwa.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG