Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Ga Gawa Daya Zuwa Biyu A Saudiyya - inji Kalarawi


Mallam Tijjani Bala Kalarawi

Yan share wuri zauna da takari suna fuskantar barazanar fatattaka daga kasar Saudiyya.

A kasar Saudiyya dai game da maganar anga takari da ‘yan share wuri zauna a cikin kuncin rikicin da ya hada da fatattakar su daga kasar Saudi. Inda har muryar Amurka ta tuntubi jakadan NAjeriya a can Saudi game da cewa har ma wasu sun rasa rayukansu.

In ba a manta bay a tabbatar mana da cewa ba wanda ya rasa ransa a cikin ‘yan Najeriya in ka dauke wani dan Nijar da aka tabbatar masa da ya bincika. Ya dai tabbatar da yanayin kunci da ake ciki ya tabbatar da cewa har da ‘yan wasu kasashen Afrikan a cikin matsalar.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi wani shahararren malami ne a Najeriya da a yanzu haka yana can yayi tafiya zuwa Saudin in da kuma ya tabbatarwa Muryar Amurka a hirarsa da Bello Galadanchi.

Malamin yace su da idon su sun ga an kewaye wani wajen da takari suke. Sannan ya tabbatar da cewa sun ga gawa daya zuwa biyu da aka dauko sun mutu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

XS
SM
MD
LG