Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 Ya Kai 8,344


Sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, sun nuna cewa wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutum 276 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 8,344 a kasar.

Jihar Legas da ke kan gaba a wajen yawan masu kamuwa da cutar ta samu karin mutum 161 da suka kamu da coronavirus, a cewar sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter.

Sauran jihohin sun hada Rivers 36, Edo 27, Kaduna 19, Nasarawa 10, Oyo 6, Kano 3, Delta 3, Ebonyi 3, Gombe 2, Abia 1, Ogun 1, Borno 1, Bauchi 1.

Ya zuwa daren ranar Laraba 27 ga watan Mayu, mutum 2,385 suka warke daga cutar, yayin da wasu su 249 suka mutu a jihohin Najeriya 34 tare da babban birnin tarayya Abuja.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG