Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: ASUU Ta Janye Yajin Aiki


Wani aji cike makil da dalibai a Jami’ar Bayero dake Kano, Najeriya. Yuni 11, 2013.
Wani aji cike makil da dalibai a Jami’ar Bayero dake Kano, Najeriya. Yuni 11, 2013.

Bayan shafe sama da wata guda tana yajin aiki, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU ta umurci malaman da su koma bakin aikinsu a yau Talata bayan wata matsaya da aka cimma da gwamnati.

Kungiyar malaman jami’o'i a Najeriya ta ASUU ta janye yajin aikin da take yi wanda ta kwashe sama da wata guda tana yi.

Amma kungiyar ta janye yajin aikin ne da kashedin cewa za a biya masu bukatunsu nan da watan Oktoba mai zuwa a cewar jaridar Punch.

Kafofin yadan labaran kasar da dama musamman ma na yanar gizo sun ruwaito shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi yana kira ga malaman da su koma bakin aiki a yau Talata.

Rahotanni sun an cimma matsaya tsakanin kungiyar ta ASUU da gwamnati ne bayan wasu jerin tattaunawa da aka yi da minisitan kwadago, Chris Ngige a jiya Litinin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar malaman ta shiga yajin aikin ne bayan da gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta 2009.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG