Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Da Alamar Arewa Na Kokarin Kaucewa Tsarin Mulkin Karba-Karba


Shugaba Buhari, dama, Sarkin Lafia, Justice Sidi Bage Muhammad 1, tsakiya da gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, hagu (Hoto: Femi Adesina)
Shugaba Buhari, dama, Sarkin Lafia, Justice Sidi Bage Muhammad 1, tsakiya da gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, hagu (Hoto: Femi Adesina)

Muhawarar mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu ba ta yi sanyi ba musamman tsakanin ‘yan manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP. Tuni jam’iyyar APC ta nuna alkibilar ta ta tura takarar kudu, biyo bayan ayyana wanda zai zama shugaban jam’iyya zai fito ne daga arewa ta tsakiya.

Duk da ita ma PDP dan arewa ta tsakiya ne ta zaba a matsayin shugaba wato Iyorchia Ayu daga jihar Binuwai, amma ta yi wata ‘yar dabarar cewa za ta bar kofar takarar a bude ga wanda ‘yan jam’iyya za su zaba ko da daga wane yanki zai fito.

Yayin da ‘yan siyasar kudu ke da matsayar lalle shugabanci a 2023 ya koma yankin su, bayan shekara 8 a arewa, mahawar ta fi tsanani a tsakanin ‘yan arewa inda wasu ke ganin daidai ne wasu kuwa na cewa a’a.

Ga tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau, tura takarar kudu ne mafi a’ala don hakan ne zai taimakawa zaman tare na Najeriya.

A na sa ra’ayin tsohon dan siyasar NEPU Alhaji Hussaini Gariko na cewa babban kuskure ne ‘yan arewa su bari mulki ya kubuce mu su ko da kuwa ba su ji dadin mulkin Buhari ba.

Duk wannan ba shi ne abun da mai sharhi kan lamuran siyasa Bashir Baba ke hangowa ba; don a tunanin sa ‘yan arewa su kan kidime in sun hau kujera.

Da alamun samun matsaya ta uku daga wata tafiyar siyasa da ke shirin zuwa ta wadanda ke ganin APC da PDP ba su yi mu su adalci ba.

Daga Abuja ga rahoton Sale Shehu Ashaka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
XS
SM
MD
LG