Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya da Morocco Sun Shiga Sakar Diflomasiyya


Sarkin Morocco Muhammad

Najeriya da Morocco sun shiga kafar wando daya sabili da abun da kasar ta Morocco ta kira karyar da Najeriya tayi mata

Najeriya ta fada wai shugabannin kasashen biyu sun yi wata ganawa ko ta ido da ido ko ta wayar tarho.

Tuni dai sarkin Morocco Muhammad ya janye jakadansa dake Najeriya yana zargin cewa Najeriya tayi masa karya. Najeriya kuma an barta da neman hanyar da zata bi ta fitar da kanta daga kunyar da ta sha a idanun 'yan Najeriya dama duniya gaba daya.

Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi wani tsohon jakadan Najeriya Lawal Munir domin ya yi fashin baki akan wannan dambarwar diflomasiya da ta kunno kai tsakanin kasashen biyu. Yace wata mahimmiyar magana ce domin duk lokacin da aka ce an janye jakada za'a yi shawara dashi ana nufin dangantaka ta kusa lalacewa ke nan.

Yace bayanai da suka fito daga Moroccon sun nuna cewa shugaban kasar Najeriya ya nemi ya kai ziyara kasar Morocco. To sai kasar tace tunda zaben Najeriya ya kusa bata son Goodluck Jonathan yayi anfani da ziyarar domin cimma wata manufar siyasa.

Ganin matsayin da Moroccon ta dauka ya sa ma'akatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da sanarwa cewa shugaban Najeriya ba zai je Morocco ba kamar yadda aka shirya domin sarkin ya tafi Faransa amma wai sun dade suna tattaunawa ta wayar tarho.

Abun damuwa shi ne yadda har kasar da bata kaita karfi ba har ta kunyatata a idanun duniya. To saidai Munir yace wadanda suka ba shugan kasa shawara ne suka haddasa lamarin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye


XS
SM
MD
LG