Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya da Nijar Sun Kafa Kwamitin Karfafa Zamantakewa da Bunkasa Kasuwanci


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kasar Najeriya da kasar Jamhuriyar Nijar suna cikin kungiyar kasashen yammacin Afirka dake da manufar inganta tattalin arzikin kasashen saboda haka wannan kwamitin da suka kafa tamkar na share fage ne da zai kaiga bude kasuwanci cikin walwala

Kwamitin zai duba hanyoyin da za’a karfafa zamantakewar jama’ar kasashen biyu da bunkasa harkokin kasuwanci da zummar taimakawa tattalin arzikinsu.

Haka kuma kwamitin zai dinga lura da shige da ficen baki saboda dakile duk wata matsalar tsaro da ka iya tasowa akan iyakokinsu.

Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou

Karamar Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim tace kafa kwamitin shi ne matakin farko na cimma manufofin da kasashen biyu suka saka a gabansu. Ministar tace Najeriya da Nijar tamkar kasa daya ne, har ta kara da cewa “mun fi kusa dasu, sun fi kusa damu”.

A cewar minister nan gaba za’a kafa irin wannan kwamitin na bunkasa harakokin kasuwanci da zumunci tsakanin Najeriya da sauran makwaftanta kamar Kamaru da Chadi, don, a cewarta, ya kamata a sami irin haka a tsakanin dukkan kasashen dake cikin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma taECOWAS.

Da yake bayyanawa wakiliyarmu Medina Dauna irin hanyoyin da zasu bi domin aiwatar da aikin,Shugaban kwamitin kuma babban darakta a hukumar dake kula da kan iyakokin Najeriya Muhammad Bosa Ahmed yace akwai bukatar a fara tunashe da jama’ar kasashen Najeriya da Nijar cewa kodayake turawa sun raba kasashen biyu amma a akasarin gaskiya al’umma daya ce.

Wakiliyar Jamhuriyar Nijar a wajen hidimar, Jakadiya Amina Jibrila Maiga ce suna fatan shugabannin kasashen biyu zasu ciwo kan matsalolin da ake fuskanta domin kasuwanci ya samu ya bunkasa.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG