Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Daga Cikin Jerin Kasashen Da Aka Fi Gallazawa ‘Yan Jarida


Kungiyar Yan Jaridu Sun Yi Zanga Zanga A Sokoto
Kungiyar Yan Jaridu Sun Yi Zanga Zanga A Sokoto

Rahotanni na cewa ana ci gaba da gallazawa ‘yan Jarida a fadin duniya, duk kuwa da irin rawar da suke takawa a ci gaban dimokaradiyya a duk duniya.

Najeriya na ‘daya daga cikin kasashen da ake gallazawa manema labarai, ‘yan jarida da a kowacce rana suke fadi tashin zakulo rahotannin ba daidai ba, tare da manufar kawo sauyi domin ci gaban al’umma, suna fuskantar nau’o’i daban-daban na cin zarafi a Najeriya.

Cin zarafin ‘yan Jarida shine makasudin wani gangami na bai ‘daya da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya ta shirya a duk fadin kasar, domin nuna turjiya da rashin amincewa da cin zarafin da ake yiwa ‘yan jarida, musamman ta bangaren jami’an tsaro da ‘yan siyasa.

Mataimakin shugaban ‘yan jarida Shehu Usman, wanda shine ya jagoranci zanga-zangar da aka gudanar a Sokoto, ya ce wajen samo labaran siyasa shine na biyu mafi hatsari bayan wajen yaki.

Kungiyar Yan Jaridu Sun Yi Zanga Zanga A Sokoto
Kungiyar Yan Jaridu Sun Yi Zanga Zanga A Sokoto

Rahotan wani kwamitin kare ‘yancin ‘yan jarida ya saka Najeriya a zaman ta 11 daga cikin jerin kasashe 12 da aka fi gallazawa ‘yan jarida a duniya.

Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG