Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Bullo Da Fasahar Kasuwanci Na Zamani Ga Matasa


Shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa Abdullah, a yayin taron NASCOS.
Shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa Abdullah, a yayin taron NASCOS.

Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta na aiwatar da manufofi da shirye-shirye da za su inganta kasuwanci na fasahar zamani domin bunkasa kananan sana’oi a tsakanin matasa, musamma daliban da ke manyan makarantu.

Darakta-Janar na hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta kasar (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na bude babban taron samar da sabbin dabaru da binciken manhajojin kasuwanci a Najeriya na shekarar 2021.

Kungiyar daliban ilimin kimiyar nau’ra mai kwakwalwa (NACOS) ce ta shirya taron, tare da haɗin gwiwar hukumomi da kamfanonin hada-hadar kudi na fasahar zamani, tare da zummar zakulo matasa masu hazaka da dabarun amfani da na’ura mai kwakwalwawajen taimakawa kasar a fagen samar da sabbin hanyoyi masu sauki.

Taron kungiyar daliban ilimin kimiyar na'ura mai kwakwalwa a Najeriya wato NASCOS.
Taron kungiyar daliban ilimin kimiyar na'ura mai kwakwalwa a Najeriya wato NASCOS.

Jami’ar Nile da ke Abuja ce ta karbi bakuncin taron da aka yi wa take da ’‘yadda za’a hada kai da matasa wajen amfani da fasahar zamani don kirkiro abubuwa na mussaman da kuma lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ci gaba a kwarewar aiki’’

Shugaban hukumar NITDA ya karfafawa matasa da su yi amfani da wannan damar wajen tallata hajarsu ta abubuwan da suka kirkiro zuwa kayayyaki da aiyukan da za'a iya kasuwanci da su.

Taron bunkasa kasuwanci ta hanyoyin fasahar zamani.
Taron bunkasa kasuwanci ta hanyoyin fasahar zamani.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro wasu shirye-shirye da dabaru da tsare-tsaren da za su taimakawa kasar da kuma ba ta damar samarwa matasa yanayin bunkasa ilimin fasaharsu da kirkirar manhajoji na cikin gida da zu taimakawa kasar.

Wadannan shirye-shiryen a cewar sa, za su samar da hanyar samun kudi ga matasa a kasar masu hazaka da basirar kirkira bayyanasu ga duniya.

Kazalika yabayyana cewa hukumarsa na aiki tukuru tare da babban bankin Najeriya da wasu hukumomin gwamnati don hada kudi ga matasa a kasar su inganta ayyukansu na kirkira, ya na mai cewa suna aiki tare da wasu jami’o'i a kasar wajen zakulo matasan.

Shigowar Annobar COVID-19 Najeriya a cewar Kashifu, ya samar da wata dama ga matasa a kasar na amfani da fasahar da su ka kirkiro wajen fara sabbin sana’oi da tallata hajarsu.

Ya ce a aikin shirin hukumar NITDAna shekarar 2021 zuwa 2024 ya fitar da tsare-tsare da matasa za su shiga don inganta ayukansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG