Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta janye tuhumar cin hancin da ta ke yi ma tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, dangane da rawar da aka yi zargin ya taka a matsayinsa na babban jami’in kamfanin makamashi na Halliburton


Tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney.

Najeriya ta janye tuhumar cin hancin da ta ke yi ma tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, dangane da rawar da aka yi zargin ya taka a matsayinsa na babban jami’in kamfanin makamashi na Halliburton.

Kafofin labarai na Britaniya sun ce Najeriya ta janye tuhumar cin hancin da ta ke yi ma tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, dangane da rawar da aka yi zargin ya taka a matsayinsa na babban jami’in kamfanin makamashi na Halliburton. Rahotanni sun ce kamfanin na Halliburton ya yarda zai biya tarar Dala miliyan 250 domin a janye wannan tuhumar. Hukumar EFCC ta ce a karar da ta shigar a makon jiya, an tuhumi Halliburton da Dick cheney da wasu jami’an kamfanin su 3 da laifin bayar da cin hanci ga jami’an gwamnatin najeriya domin a ba su kwangilar gina masana’antar sarrafa man gas a yankin Niger Delta. Kafofin labarai na Najeriya sun ce tsohon shugaban Amurka George H. W. Bush babba, da tsohon sakataren harkokin waje James Baker, sun taka rawa wajen ganin an janye wannan tuhumar. Kamfanin Halliburton bai ce uffan ba game da yarjejeniyar sasantawar da aka ce ya kulla da Najeriya.

XS
SM
MD
LG