Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kara Austria, Sweden a Yaki Da Coronavirus


Wani ma'aikacin lafiya yana kulawa da wani mai tutar coronavirus a Italya, asaya daga cicin kasashen da Najeriya ta hana su shiga kasar
Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumomin kasar sun kara Austria da Sweden a jerin kasashen da suka haramtawa shiga kasar, a kokarin da suke yi na dakile yaduwar cutar coronavirus.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana daukan wannan mataki a karshen makon nan a Abuja.
Cutar coronavirus wacce ta fara bulla a China, ta karade kusan dukkan sassan duniya.
Yanzu adadin kasashen da Najeriyar ta hana matafiyansu shiga kasar ya kai 15, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A makon da ya gabata, hukumomin kasar suka saka takunkumin shiga kasar ga kasashen China, Italiya, Korea ta Kudu, Spain, Japan da Jamus.
Sauran sun hada da Amurka, Faransa, Norway, Burtaniya, Netherlands da kuma Switzerland.
Jaridar Vanguard ta ce hukumomin Najeriyar sun dauki wannan mataki ne lura da yadda cutar ta ke kara bazuwa a kasashen na Sweden da Austria.
Ya zuwa ranar Juma'a, alkaluma sun nuna cewa Austria na da mutuum 2,333 da suka kamu da cutar yayin da Sweden ke da mutum 1,456.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG