An sanya hannu kan yarjejeniyar da kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC a Abuja don samar da wutar a cibiyar da a ka kebe a yankin Gwagwalada.
Wannan tallafi da aikin bunkasa mu’alar cinikaiya na hukumar ta Amurka ya kara bunkasa a rubu’in karni a bangaren iskar gas a kasashen duniya.
“Mun taimakawa aiyuka da dama, kamar bunkasa cin gajiyar iskar gas ta hanyar bincike, kwarewar fasaha da ciniki” inji shugaban hukumar bunkasa kasuwancin ta Amurka, Mista Thomas Hardy.
Baya ga Najeriya a yanzu, wasu kasashen da irin wannan yarjejeniyar ta shafa sun hada da Lithuania da Turkiyya da Goegia da Aljeriya da kuma India.
Hardy, ya kara da cewa “abun da na lura da shi, shi ne sirrin nasarar mu, shi ne samun abokan hulda da su ka cancanta”
Hukumar za ta turo kudin ne a kashi-kashi har ta kammala bayarwa, don wannan aiki da zai kara inganta lantarki a Najeriya da ke cikin kasashe na kan gaba da ke huldar diflomasiyya da kasuwanci da Amurka a nahiyar Afirka.
Shugaban kamfanin Man fetur na Najeriya NNPC, Mele Kyari Kolo ya ce wannan zai tallafa wajen amfana daga iskar gas da ta ke hanya mafi sauki ko rashin tsada wajen samar da hasken wutar lantarki.
Kyari Kolo, ya kara da cewa aikin zai kara rage yadda Najeriya ke asarar iskar gas don rashin amfani da ita ga aiyuka masu riba.
Kafin batun wannan aiki na iskar gas, an shafe fiye da shekaru 40 a na batun wutar daga ruwa a tsaunin Mambilla mai karfin Megawatt 3,050 da zuwa yanzu an ga jami’an aikin daga China suna duba aikin.
Wazirin Mambilla Sanata Bashir Marafa, ya yi fatan gwamnatin Buhari za ta dage don kammala aikin kafin kammala wa’adi a 2023.
Gwamnati dai ta baiyana aikin zai lashe Naira tiriliyan 2.1 wato ta samun lamunin kudin da su ka kai dala biliyan 5.495 daga bankin EXIM na kasar China.
Don cikkaken rahoton saurari wakiliyar muryar Amurka Hauwa Umar:
Facebook Forum