Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulki a Guinea


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

A watan Oktoba shugaba Alpha Conde ya lashe zabe a karo na uku bayan da ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, abin da ya ba shi damar sake tsayawa takara duk da cewa ya kammala wa’adinsa na biyu.

Najeriya ta yi kira ga sojojin kasar Guinea da suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde da su yi maza su janye matakin da suka dauka.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta Esther Sunsuwa, ta ce, juyin mulkin da dakarun kasar suka yi, ya sabawa tsarin dimokradiyya da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO take karewa.”

“Gwamnatin Najeriya, na bakin cikin wannan juyin mulki da aka yi a Jamhuriyyar Guinea a yau (Lahadi), matakin da ya sabawa tsarin dimokradiyya da kungiyar ECOWAS take mutuntawa.

“Gwamnatin Najeriya na Allah wadai da wannan juyin mulkin da kakkausan harshe, tana kuma kira ga wadanda ke da hannu a wannan lamari, da su mayar da kasar mai bin kundin tsarin mulkin ba tare da bata lokaci ba, su kuma kare rayuka da dukiyoyi.”

A ranar Lahadi wasu sojojin kasar suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Conde a wani jawabi da suka yi ta kafar talabijin.

Sojojin sun yi ikirarin cewa gwammatin Conde na tafiyar da al’amuran kasar ta hanyoyin da ba su dace ba.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san inda shugaba Conde yake ba.

Amma wasu hotunan da kamfanin dillancin labaran AFP suka fitar, sun nuna Conde a zaune a wata kujera da kayan jikinsa duk a yamutse yayin da sojoji ke zagaye da shi.

A dai watan Oktoba shugaban ya lashe zabe a karo na uku bayan da ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, abin da ya ba shi damar sake tsayawa takara duk da cewa ya kammala wa’adinsa na biyu.

Wannan mataki ya haifar da rudani da zanga-zanga a duk fadin kasar.

XS
SM
MD
LG