Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Fara Hukunta Matafiyan Da Suka Bijirewa Dokar Coronavirus


Wani jirgin Ethiopia a filin tashin jirage na Abuja, babban birnin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta fara farautar wasu mutane 90 da suka hada da 'yan Najeriya da kuma baki da suka karya dokar killacewa don annobar coronavirus bayan shiga kasar daga kasashen Indiya da Turkiyya da kuma Brazil.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin kasar, kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus da shugaba Buhari ya kafa, Boss Mustapha.

Manajan kota kwana na kwamitin yaki da cutar coronavirus Dr. Mukhtar Muhammad, ya ce an sa dokar hana shigowa da kuma killacewa bayan shigowa Najeriya ne domin kare lafiyar 'yan kasar da kuma tabbatar da lafiyar masu shigowa kasar.

Dr. Mukhtar ya kara da cewa gwamnati ta tanadi hukunci da za a yi wa duk wadanda suka karya dokar da ya hada da kwace passport na tafiye-tafiye ga 'yan Najeriya da kuma kwace visa ko takardar shaidar zama a kasar ga wadanda ba yan Najeriya ba.

A nashi bangaren, kakakin hukumar shige da fice ta Najeriya James Sunday, ya ce hukumarsu na taka rawar gani wajen amfani da na'urorin dake tantancewa da kuma zakulo duk wadanda suka shigo kasar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Domin karin bayani saurari rahotan Hauwa Umar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG