Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Jagoranci Taron Kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa Na Duniya


Wata tashar jirgin ruwa da ke California a Amurka

A karon farko an shirya gudanar da taron Kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa Na Duniya a Najeriya, taron wanda a karon farko Ake gudanar Dashi a wata nahiya daba ta Turai zai duba hanyoyin bunkasa sufurin Jiragen ruwa tare da kasuwanci da tsaron tekunan duniya.

Taron da za a gudanar karo na farko a nahiyar Afirka, a zai yi nazari akan hanyoyin bunkasa safarar kayan da ake shigowa da su kasashen yankunan da babu tashoshin ruwa ta hanyar amfani da mota da kuma jiragen kasa.

Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya Hajiya Hadiza Bala Usman, wacce ita ce mataimakiyar wannan kungiyar, ta ce taron shine na farko da aka shirya za’a gudanar a Nahiyar Afrika.

Haka-zalika kakakin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan ya bayana cewa mukasudin wannnan taron shine don a duba yadda za’a rika safarar kayan da ake shigowa da su daga Turai zuwa cikin kasa ko wasu kasashen da basu da tashoshin jiragen ruwa domin samun riba.

Shugabar Hukumar Tashohin Jiragen Ruwa Hajiya Hadiza Bala Usman, ta yi Karin bayani, cewa “kokarin da hukumar take yi na safarar kayan da ake shigowa da su dake kasashen waje zuwa yankunan arewacin Najeriya, ya zama dole a yi amfani da jirgin kasa, wajen kwasar kayan daga tashoshin jiragen ruwa zuwa cikin kasa, ta haka ne kawai za’a samu ragewar cinkoso kuma a samu biyan bukatar gudanar da kasuwanci”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG