Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Nemi Amincewar Duniya a Jawo Ruwa Zuwa cikin Tafkin Chadi


Suleiman Husseini Adamu Ministan Albarkatun Ruwa na Najeriya

A zantawar da yayi da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka ministan albarkatun ruwa na Najeriya yace akwai bukatar kasar ta nemi amincewar kasashen duniya a jawo ruwa zuwa cikin tafkin Chadi domin ya sake farfadowa

Injiniya Suleiman Useni Adamu, ministan albarkatun ruwa na Najeriya y ace babu yadda za’a warware matsalar bushewar tafkin Chadi sai Najeriya ta nemi amincewar duniya a jawo ruwa zuwa tafkin.

Yace ya je wani taro a Birnin Paris a kasar Faransa dangane da batun. Zasu shirya babbar muhawara da kwararru domin a jawo ruwan zuwa tafkin.

Alhaji Bababo Abba dan masani Fika wanda ya taba zama babban sakataren raya kogin Kwara mai kasashe takwas dake da alaka da tafkin Chadi yace lokacin da tafkin Chadin yak e nan ba wuri ba ne na su kawai har masu yawon bude ido na zuwa wurin. Halin da tafkin ka ciki, Najeriya ita kadai ba zata iya gyarashi ba. Y ace wajibi ne ta samu amincewar duniya gaba daya a taron duniya da ake yi akan albarkatun ruwa saboda tafkin ya shafi kasashe bakwai.

Baicin batun tafkin Chadi, ministan y ace akwai wani sabon shirin yawaita Birnin Maiduguri da ruwa

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG