Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Samu Tallafi Daga Turai


Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda
Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda

Kungiyar kasashen turai zasu taimakawa jihohin Najeriya

Kungiyar kasashen turai zata bada tallafi wa jihohin Najeriya a fannonin dasuka hada dana kiwon lafiya,ayyukan gona dakuma bunkasa wutan lantarki.

Jakadan kungiyar kasashen turai a Najeriya Mr.Mishell Areon ne ya furta hakan a lokacin daya kai ziyarar yini guda jihar Bauchi.

Yace dangane da aiyuka tamakon da suke gudanarwa tuni sun fara aiyukan kiwon lafiya tun daga tushe a jihar Bauchi irin su alluran riga kafi masamman na uwa da jaririta, abuna biyu shine bunkasa aiyukan gona da samarda wutan lantarki.

Shima gwamna jihar Bauchi malam Isa Yuguda yayi Karin haske da kuma bayana fatan samun wadannan taimako daga kungiyar kasashen Turai kamar yanda jakadan ya furta.

Ya kuma ce “ yayi alkawura dayawa don abunda yasama suka bude ofishin a Najeriya shine a matsayin sun a matsayin sun a kungiyar kasashen turai su samu yanda zasu taimakawa nahiyar Afirka masamman kasa kamar Najeriya wanda take da yawan jama’a."
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG