Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nakasassu Yan Jam’iyyar PDP Sunyi Wata Zanga Zangar Lumana


PDP
PDP

Kungiyar nakasassu magoya bayan jamiyyar PDP a Najeriya ta gudanar da zanga zangar lumana a sakatariyar jamiyyar na kasa a Abuja, bisa yadda sukace ana nuna masu banbanci.

Hon Abdullahi Jigunu, shine shugaban kungiyar nakasassu magoya bayan jam’iyyar PDP a Najeriya, wanda yace shugaban PDP na kasa baki daya bai san waye nakasassu ba, duk da sunyi kokari an saka sunansu a cikin wadanda zasu je babban taron jam’iyyar da za a gudanar a jihar Port Court, amma yanzu babu sunansu ko daya kuma wannana daliline yasa suka fito domin nuna damuwarsu.

Ya kuma kara da cewa yanzu haka sun sami ganin shugaban jam’iyyar, inda ya nemi da su kai masa bukatun da suke dasu.

Mai magana da yawun shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Mr Inuwa Gwala, yace Modu Shariff ba shi bane mai zaben wakilan da zasu je babban taron da za a yi ba, kwamitine ke gudanar da wannan ayyukan.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00

XS
SM
MD
LG