Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FBI Ta Ce Nakiya Ce Ta Fashe Cikin Masallaci a jahar Minnesota.


Musulmi a masallacin Abubakar As Saddique dake birnin Minneapolis.
Musulmi a masallacin Abubakar As Saddique dake birnin Minneapolis.

Babu wanda ya jikkata sakamakon bindigar da tayi a cikin masallacin da ake kira Dar al-Farooq.

A Minnestota, wani jami'in FBI yace wata nakiya ce hadin gida tayi sanadiyyar fashewa data auku jiya Asabar a wani Masallaci da ake kira Dar-al-Farooq dake birnin Bloomington.

Babu wanda ya ji rauni sakamkon wannan fashewa.

Jami'in na FBI Rick Thornoton,wanda shine jagoran masu binciken musabbabin wannan fashewar, ya gayawa manema labarai jiya Asabar din cewa, " a wannan marra, abunda muka fi maida ha kali akai shine tabbatar da wanene ya dasa ta, kuma saboda me," ya kara da cewa "Wannan hari ne na ta'addanci? shine abunda wannan bincike zai gano."

Darektan masallacin Mohammed Omar, ya gayawa sashen Somalia na na Muriyar Amurka cewa, daya daga cikin masallatan ya ga wani mutum cikin wata mota akori kura aharabar maslalacin, kuma sai tayu yana da hanu a fashewar.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 5 na asubah agogon tsakiyar Amurka, watau misalin shida agogon Washington, karfe 11 na safe agogon Najeriya, Nijar Cadi da kamaru, watau 10 na safe agogon Ghana

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG