Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NATO Ta Zo Karshen Faretin Jiragen Mayakanta Na Ruwa A Somalia


Jami'in sojin Amurka ya cafke barawon teku a Somalia.
Jami'in sojin Amurka ya cafke barawon teku a Somalia.

Rundunar sojan Turai ta NATO tace ta zo karshen shirin nan da ake kira da turanci “Ocean Shield” na faretin jiragen mayakanta a cikin teku don tinkarar barayin teku na Somalia masu zirga-zirga cikin tekuna.

Wannan shirin da ya hada tarin jiragen ruwan yaki na kasashen duniya da dama da suka hada da na Amurka da Turai, na daya daga cikin matakan da suka samu nasara da aka dauka don maganin masifar barayin teku da suka addabi mutane a wasu shekarun baya.

A lokacinda barayin tekun ke shake ayarsu a can baya, ance sun saci dukiyar da ta kai ta zunzurutun kudi kamar Dala milyan dubu 7, kuma sunyi garkuwa da mutane sunfi dubu daya.

To amma rahottani sunce yanzu abin ya ragu matuka, don rabon da ace anyi wata gagarumar sata a cikin teku tun shekarar 2012; wannan ragi ne babba idan aka yi la’akari da cewa tsakanin shekarun 2010-2011, an kai farmaki akan jiragen ruwa sun fi 30.

Yanzu rahottani sunce NATO zata maida hankalinta ne zuwa tekunan Bahar Aswad da Mediterranean don tinkarar Rasha da kuma masu aiyukkan fasa kwabri a cikin tekunan.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG