Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NATO Tana Binciken Ikirarin Harbo Jirgin Da Taliban Ta Yi


Jirgin yakin helkwafta samfurin Chinook CH-47 a Afghanistan

Zaratan sojojin Amurka 30 da na Afghanistan su 7 suka mutu a wannan hasarar rayuka mafi yawa da NATO ta taba yi a hari guda tun fara yakin Afghanistan shekaru 10 da suka shige

Kungiyar tsaron NATO tana binciken ikirarin da Taliban ta yi cewar ita ce ta harbo wani jirgin helkwafta na sojojin Amurka a tsakiyar Afghanistan har ta kashe mutane 38, cikinsu har da zaratan sojojin Amurka.

An ci gaba da gwabza fada yau lahadi a lardin Wardak inda wannan helkwafta samfurin Chinook CH-47 na sufurin dakaru ya fadi daren jumma’a. Sojojin Amurka 30, cikinsu har da ‘yan rundunar zaratan nan da ake kira Navy Seals, sun mutu tare da sojojin kundumbala 7 na Afghanistan da wani tafinta guda daya.

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa ita ce ta harbo jirgin. Dakarun gwamnatin Afghanistan a wurin sun ce helkwaftar ta fado ne a bayan da aka harbe ta da roka. Wannan lamarin ya faru a bayan wani farmakin da Amurka ta jagoranci kaiwa a kan wani gida na ‘yan Taliban da aka gano inda aka kashe tsagera 8.

Wannan ita ce hasarar rayuka mafi muni a hari guda da sojojin kawance suka fuskanta tun lokacin da aka fara yakin Afghanistan kusan shekaru goma da suka shige.

A wasu jawabai dabam-dabam, sakataren tsaron Amurka Leon Panetta da sakatare janar na kungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen sun ce sojojin kawance zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu a Afghanistan. Kungiyar NATO ta fara mayar da hakkin ayyukan tsaro ga sojojin Afghanistan a wasu sassan kasar, a wani bangare na shirin janye dukkan sojojin kai farmaki na NATO nan da karshen shekarar 2014.

A wani sabon tashin hankalin dabam kuma, NATO ta ce an kashe mata sojoji 4 yau lahadi a wasu hare-hare guda biyu na ‘yan tawaye a kudancin Afghanistan da kuma gabashin kasar.

XS
SM
MD
LG