Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NCAA Zata Tantance Lafiyar Jiragen Saman Da Ake Amfani Dasu A Cikin Najeriya   


Jirgin kamfanin Dana Air da kauce daga kan hanyarsa a filin saukan jiragen sama a Legas.
Jirgin kamfanin Dana Air da kauce daga kan hanyarsa a filin saukan jiragen sama a Legas.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a wani shirin tashar talabijin ta Channels na jiya alhamis mai taken “Politics Today” a turance.

WASHINGTON DC - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewar Hukumar NCAA mai kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya zata gudanar da cikakken bincike akan jiragen saman da ake amfani dasu a cikin kasar.

Ya kara da cewar baya ga dakatar da ayyukan kamfanin jiragen saman Dana da kuma aikin tantance lafiyar jiragen saman da ake zirga-zirga dasu, za’a gudanar da bincike akan duk wani kamfanin jirgi dake aiki a kasar nan domin kiyaye lafiyar fasinjoji dama harkar sufurin jiragen saman baki daya.

A Larabar da ta gabata ne, Keyamo ya umarci Hukumar NCAA ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin saman Dana, inda yace abubuwan da suka same shi a baya-bayan nan sun jawo matukar damuwa game da tsare-tsarensa na kiyaye afkuwar hatsura dama karfin jarin gudanar da harkokinsa.

Ministan yace kamfanin jirgin saman zai cigaba da kasancewa a dakace har sai an gudanar da cikakken bincike akansa, umarnin da Babban Daraktan Hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ya aiwatar nan take.

An aiwatar da hukuncin dakatarwa akan kamfanin Dana Air sa’o’i 24 bayan da daya daga cikin jiragensa ya kauce daga kan hanyarsa a filin saukar jiragen saman Legas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG