Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDLEA Ta Yi Wawan Kamu a Jihar Ogun


NDLEA LOGO
NDLEA LOGO

Hukumar dake yaki da sha, safara da ta'ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya ko NDLEA reshen jihar Ogun ta kama motocin daukan kudi biyu shake da tabar wiwi da kudinsu ya kai nera miliyan 30.

Alhaji Musa Bala Fagge kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar yace a makon da ya wuce sun kama motoci biyu irin masu daukan kudi shake makil da tabar wiwi.

Daya an zuba buhu ashirin a cikinta. Dayar kuma na dauke da buhu ashirin da daya.

Ana kyautata zaton mota daya zata arewa daya kuma nan jihar Ogun zasu da ita. Bayan wadan nan motocin da suka kama sun shiga bincike domin su san daga ina ake dauko tabar. Sun ci sa'a sun tafi wani kauye can kasar Jabu inda suke dauko tabar inda suka samu lodin tabar wiwi buhu 382.

Sun dauko 232 sannan suka kona buhu 150 a wurin. Kudin tabar da suka maka zai kai kimanin nera miliyan 30 zuwa 35.

Game da tabar sun kama mutane guda shida amma sun cigaba da binciken kwakwaf su gano wadanda suka ta'ammali da kamun da suka yi.

Kalubale babba da hukumar ke fuskanta shi ne rashin kayan aiki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG