Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu ya jajantawa Palasdinawa


Benjamin Netanyahu

Ana zargin wasu ‘yan share wuri zaunan Yahudawa da laifin kone wasu gidaje biyu a inda aka fi sani da West Bank da Isra’ila ta yi kaka gida.

Inda wani jaririn watanni 18 da haihuwa ya kone kurmus tare da wasu mutane hudu daga zuri’ar gidajen. Daruruwan mutane sun shiga cikin jerin gwanon yin Allah wadai, sannan ana hatsaniya a wurare sakamakon bullar labarin mutuwar jaririn.

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi wayar da ba kasafai ya cika yiwa shugaban kasar Palasdinu Mahmud Abbas ba. Inda ya nuna cewa, wannan harin cikin dare bai kamata ba kuma abin takaici ne da ban tsoro. Sannan ta’addanci ne ta ko wane bangare aka auna abin.

Mista Netanyahu yace Isra’ila tana yaki da ta’addanci ba tare da yin la’akari da duk wanda ya aikata ba. Kungiyar Palasdinawa (PLO) ta lafta laifin akan Netanyahu da suka ba ’yan kaka gida wajensu suka zauna. Yayan jaririn dan shekaru da iyayen suna kan jinyar konewar jikinsu.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG