Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEW YORK: Taron Shugabannin Majalisun Dokokin Kasashen Duniya


Yakubu Dogara, Kakakin majalisar wakilan Najeriya

Kungyar majalisun dokokin kasashen duniya ta shirya taron shugabannin majalisun a karkashin Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Daya daga cikin wadanda suke halartan taron a Majalisar Dinkin Duniya shi ne Yakubu Dogara kakakin majalisar wakilan Najeriya.

Abokin aiki ya samu ya zanta da Yakubu Dogara saboda samun bayani akan makasudin taron, wato dalilin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta gayyatosu.

Batun Dimokradiya shi ne yake kan gaba. Akwai batun 'yanci musamman na nakasassu da mata da matasa da yara. Musamman taron ya karkata hankalinsa ne akan yadda za'a mori dimokradiya a samu zaman lafiya a duk fadin duniya. Abu dake biye da wannan kuma shi ne samun cigaba dawamamme saboda a samu duniya da al'umma ke sha'awa.

Dangane da ta'adanci taron ya amince abu ne da ya addabi duniya duka. Saboda haka bai kamata a dorawa kasa daya hakin yaki da ta'adanci ba. Kamata ya yi ya zama abu na hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya su yaki ta'adanci a koina ya yi katutu.

Gina kasa ma ba na gwamnatin kasashe kadai ba ne. Yakamata hakin ya rataya akan majalisu domin su ma su kawo irin nasu tallafin kan yadda za'a shimfida dokokin da zasu taimaka wurin gina duniyar.

Bisa ga bayanin Kakaki Yakubu Dogara an tambayeshi irin rawar da 'yan majalisar wakilan Najeriya zasu iya takawa bayan kafa dokoki. Sai yace kowa ya san aikinsu ne su kafa dokoki kuma a wurin taron an nanata masu su kafa dokoki a kasashensu da zasu taimaka wajen gina duniyar da mutane ke sha'awa.

A matsayinsu na wakilan mutane Kakaki Dogara yace zasu fadakar da mutane akan abun da yakamata a yi. Hakinsu ne su yi bincike tare da matsawa gwamnati ta bi doka. A Najeriya ban da cin hanci da rashawa da talauci akwai rashin bin doka da ya addabi kasar.

Idan al'umma ta ga gwamnati na bin doka su ma zasu bi doka. Hakin majalisa ne ta tabbatar gwamnati ma kanta ta bi doka saboda cimma burin gina kasa mai zaman lafiya.

Najeriya kasa ce da yakamata tana da rundunonin 'yansanda daban daban ba daya ba kawai kamar yadda ake dasu nan Amurka kala kala kowacce da nata aikin.

Yakubu Dogara yace a jam'iyyarsu sun yadda za'a kawo canji domin akan shi ne suka ci zabe. Idan rundunar 'yansandan Najeriya bata isa ba ya zama masu wajibi su canza tunane domin su cika alkawarin da suka yi. Idan ta kama a kafa wasu rundunoni na 'yansanda ba zasu ki yin hakan ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:41 0:00

XS
SM
MD
LG