Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

New Zealand Za Ta Haramta Amfani Da Wasu Nau'ukan Bindigogi


Firai Ministar New Zealand, Jacinda Ardern da wasu shugabannin addinin Islama a Wellington, Maris 19, 2019.

Kasar New Zealand, ta fara daukan matakan dakile hare-haren ta'addanci da akan kai ta hanyar haramta amfani da wasu nau'ukan makamai.

Kusan mako guda bayan da aka halaka Musulmi 50 da ke ibada a wasu masallatai a garin Christchurch da ke New Zealand, Firai Ministar kasar, Jacinda Ardern, ta ce za a haramta amfani da duk wata nau’in bindiga mai sifar bindigogin da sojoji ke amfani da su, wadanda sukan iya sarrafa kansu.

A yau Alhamis, Firai Ministar wacce ta bayyana wannan mataki a Wellington, ta kara da cewa, za a kuma haramta amfani da bindigogin da ke da kunshin-kunshin harsashai da kuma irin sassan da akan dasawa bindiga domin ta kara saurin yadda harsashai ke fita.

Ardern ta kuma bayyana wani tsari da za su fitar, wanda zai saye makamai daga hannun wadanda suka mallaki irin wannan bindiga.

Harin na New Zealand, ya haifar da mummunan suka daga sassan duniya musamman ma daga kasashen Musulmi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG