Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neymar ya Ceto Yaron da ya Garzaya Cikin Fili a Afirka ta Kudu - 06/03/14


Neymar na Brazil dauke da wannan yaro zai kai shi wurin 'yan wasan kasar Brazil
Neymar na Brazil dauke da wannan yaro zai kai shi wurin 'yan wasan kasar Brazil
Haka kwatsam aka ga yaron ya sheka cikin fili, har jami'an tsaro sun kora shi zasu yiw aje da shi sai Neymar yace a kyale shi.

Watau kallon wasan kwallon kafa na kasar Brazil a lokuta da dama su kan sanya mai sha'awar tamaula yayi wasu abubuwan da bai saba yi ba, komai girmansa. Balle ma dai a ce yaro ne wanda ko shekara goma bai kai da haihuwa ba.

Abinda ya faru ke nan laraba a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu, a lokacin da ake gudanar da wasan sada zumunci a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil da takwararta ta Afirka ta Kudu.

A lokacin da wannan yaron ya ga gwarzayensa a filin wasa, kawai sai aka gan shi ya sheka cikin fili da gudu. Masu gadi da suka gan shi sun tare shi kuma suka dauke shi zasu fitar da shi domin kada ya tsayar da wasa.

Ganin haka sai gwarzon kwallon kafar Brazil Neymar ya sanya baki a kan a kyale wannan yaron. Neymar ya dauki wannan yaron a hannun ya je ya gabatar da shi ga sauran 'yan wasan Brazil, ya gaisa da kowa, suka kuma sanya shi a tsakiya su na jefa shi sama su na cafkewa su na masa wasa.

Daga bisani kuma sun dauki hoto shi da Neymar.

Neymar dai ya jefa kwallaye har 3 a wannan wasa inda Brazil ta doke Afirka ta Kudu da ci 5 da babu.
XS
SM
MD
LG