Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansanda A Najeriya Tana Neman Kananan Yaran Makaranata Da Ake Garkuwa Dasu.


Unidentified policemen on guard duty to provide security against kidnapping rings in Nigeria. (File Photo)
Unidentified policemen on guard duty to provide security against kidnapping rings in Nigeria. (File Photo)

'Yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba,sun sace wata motar safa dauke da yara 'yan makaranta,da aka sace kan hanyarsu zuwa makaranata a cikin jihar Abia.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya tana neman wadansu kananan yara ‘yan makaranta guda goma sha biyar da ‘yan bindiga suka sace a kudu maso gabashin kasar.

Yan sanda sun bayyana Talata cewa,‘yan bindigan sun yi fashin motar safa da yaran ke ciki, suka kuma nemi a biya su dala dubu dari kudin fansa,(kusan Naira milyan ashirin).Kamar yadda jami’an suka bayyana,an sace yaran ne ranar Litinin da safe kan hanyar zuwa makarantarsu da ake kira Abayi International,dake jihar Abia.

An yi fama da sace sacen mutane domin neman kudin fansa a jihar,dake kusa da yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya.

Da farko akasarin garkuwa da jama’a da ake yi a yankin Niger Delta ya shafi ma’aikatan man fetir ne kawai, sai dai a baya bayan nan, maharan sun fara satar kananan yara da kuma dangin attajiran kasar.

Ana sakin akasarin wadanda aka sace ba tare da sun jikkata ba, yawanci bayan biyan kudin fansa.

XS
SM
MD
LG