Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nigeria ta fara zaman makokin kwanaki uku


yan sanda a wurin da jirgi saman DANA yayi hatsari a ranar Lahadi)

An fara makokin kwanaki ukun wadanda hatsarin jirgin sama ya rutsa da su jiya Lahadi a Lagos, daukacin fasinjojin jirgin saman 153 sun mutu.

An fara makokin kwanaki ukun wadanda hatsarin jirgin sama ya rutsa da su jiya Lahadi a Lagos, daukacin fasinjojin jirgin saman 153 sun mutu.

Har ya zuwa safiyar Litinin din hayaki na tashi daga cikin mushen jirgin saman a daidai lokacin da ma’aikatan ceto ke kwasar gwarwakin da kuma kawar da buraguzan gine-ginen da jirgin ya fadawa.

A cikin tattaunawar da Muryar Amurka ta yi da mai ba shugaban Najeriya shawara Reuben Abati, ya ce za a yi riga malam masallaci idan an ce ga musabbabin faduwar jirgin saman.

Yace abun da shugaban Nigeria fa kara yi, shi ne bada umarnin gudanar da bincike nan take don a gano musabbabin hatsarin. A saboda haka Reuben Abati yace ya kamata a dakata, a jira sakamakon binciken. Yace haka kowa ya na firgice, har da shugaban kasar, yanzu dai abun da ke gaban kowa, shi ne jama’ar da ke juyayi.

Jami’an hukumar jiragen sama ta Najeriya sun ce jirgin saman kamfanin Dana ya taso daga Abuja za shi Lagos ya fadi kan wani gini mai hawa biyu a wani wuri mai cunkoson jama’a, kuma hatsarin ya sa wasu gine-ginen da ke waje-wajen sun kama da wuta.

Har yanzu babu tabbas game da adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su a kasa. Jami’an hukumar jiragen saman sun ce jim kadan kafin jirgin saman ya yi kasa matukin ya tuntubi hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Lagos ya sanar da cewa ya samu matsalar gaggawa.

XS
SM
MD
LG