Accessibility links

Najeriya Ta Doke Zambia Da Ci Daya Da Babu.

  • Aliyu Imam

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa Najeriya suke addu'a kamin a fara wasa.

Wannan Ya baiwa kasar damar zuwa wasan kwallon kafa na cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Yanzu nan ne aka tashi daga wasan kwallon kafa tsakanin Najeriya da Zambia domin samun zuwa gasar cin kofin duniya da za'a yi a shekara ta 2018.

Najeriya ta doke kasar Zambia da ci 1-0, a wasan da aka yi a fili wasannin Najeriya dake Uyo.

Dan wasan gaba na Arsenal Alex Iwobi shine ya saka kwallon da ya baiwa Najeriya galaba a daidai minti sba’in da uku da yin wasan

Najeeriya itace kasar Afrika ta farko da ta fara samun tikitin shiga gasar cin kopin duniyar da za a yi a Rasha shekara mai zuwa duk da yake a kwai ragowar wasa daya a rukunin na B.

Nasara da Najeriya a wannan wasa ya kara rata da maki goma sha uku tsakaninta da Zambia wacce take biye da ita da maki bakwai a cikin rukunin, hakan na nuni babu wata kungiya na rukunin da zata kamo Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG