Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: An Bude Wata Sabuwar unguwa A Yankin Tilabery


Ambaliyar ruwa a Nijar

A wani yunkurin kare al’umar kauyen Borgo dake yankin Tilabery daga barazanar ambaliyar ruwa kungiyar quatar Charity ta gina masu wani gari mai gidaje 100 wadanda suka tanadi wutar lantarki hade da fomfuna da dukkan wasu kayayakin bukatun iyali.

Sau biyu jere ambaliyar ruwa ke ruguza gidajen al’umar kauyen Borgo ta gundumar Balleyara lamarin da ake alakantawa da rashin dacewar filin da aka tsara garin tun farko. Daliki i ke nan da kungiyar Quatar Charity ta yanke shawarar gina wani gari sabo ful mai gidaje 100 da nufin kawo karshen wannan matsala.

Ministan cikin gida Bazoum Mohamed wanda ya jagoranci bukin damka wadanan gidaje a hannun wadanda aka yi domin su, ya jinjinawa wannan kungiya saboda a cewarsa ta yi abinda ya kamata takwarorinta su yi koyi da shi.

Wadanda Sashen Hausa ya yi hira da su, a wajen kaddamar da gidajensu sun bayyana frin cikinsu, da cewa suna daukar bukin damka wadanan gidaje tamkar wata ranar salla.

Seini Issoufou daya daga cikin wadanda suka ci moriyar wannan tallafi, yace “Ina godiya da muka samu wannan alheri a cikin garinmu. Ina yiwa Allah godiya kuma ina godewa wadanda suka yi dalilin samun wannan taimako. Mun yi murna sosai.”

A watan mayun 2017 ne kungiyar Quatar Charity ta kaddamar da wannan aiki dake matsayin na gwaji wanda kuma aka bayyana cewa ya lakume miliyan 1200 na cfa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumoni Barma

Bukin mika gidaje a Nijar-2:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG