Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: An sake yin zanga zangar kin jinin juyin mulki


Hoton zanga zangar kin jinin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Hoton zanga zangar kin jinin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Daruruwan mutane sun sake gudanar da wani gagarumin gangamin kin jinin yunkurin juyin mulki da ake zargin wadansu sojoji da yi a Jamhuriyar Nijar.

Zanga zanga da aka gudanar a birnin Kwanni ta kunshi ‘yan siyasa, sarakuna, malamai, ‘yan boko, ma’aikata, kungiyoyin farar hula da sauransu. Sun yi tururuwa ne a ajerin gwanon yin Allah wadai a yunkurin juyin mulki da kuma yunkurin hallaka shugaban kasa a cikin wannan watan. Yanzu haka dai ana tsare da sojoji da ake zargi da wannan yunkurin.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Alhaji Zakari Umaru Dan majalisar dokoki, wanda kuma shine shugaban rukunin ‘yan majalisa da jam’iyar PNDS Tarayya, mai wakiltar birnin Kwanni, yace yunkurin juyin mulki koma baya ne a damokaradiyar kasar.

Sai dai a nasu bangaren ‘yan hamayya sun bayyana cewa, basu ga wani abu ba da yayi kama da kare damokaradiya a wannan zanga zangar. Bisa ga cewarsu, kamata ya yi a ba kowa irin wannan damar, ta bayyana ra’ayi amma ba bangare guda kadai ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Mamman Bako ya aiko daga birnin Kwanni, Jamhuriyar NIjar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG