Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Nijar: Dokar Yi Wa Mutane Kutse Na Janyo Ce-ce Ku-ce


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Wata doka wacce za ta bai wa hukumomi a Nijar damar sauraren dukkanin hirarrakin wayoyin da mutane suka yi da kuma sakkonin da suka aika a shafin intanet na ci gaba da janyo ce-ce ku-ce.

‘Yan hammaya a Nijar sun bayyana damuwa dangane da abin da suka kira yunkurin rufe bakin ‘yan kasa.

Bangaren zartarwa dai tuni har ya gabatar wa majalisar dokokin kasar kudirin dokar da ke hangen bai wa gwamnatin ‘yancin yin kutsen, a yayin da bangaren masu rinjaye suka ce an yi wa dokar mummunar fahimta ne.

Alhaji Ibrahim Yacouba shi ne shugaban jam’iyyar MPN kishin kasa ta kawancen Front Patriotique, “dokar kasar nan ta hana a bai wa mutane izinin leken bayanan sirin kowa, sai ga shi yau gwamnati ta aiko da wannan dokar.”

“Lokacin da kawai dimokraddiya ta ba da izinin a yi watsi da wannan dokar shi ne idan shari’a ta gano cewa mutum yana kokarin kulla wani abu mara kyau.”

Sai dai a cewar dan majalisar dokokin kasa na jam’iyar PNDS TARAYYA madugar jam’iyyu masu mulki Hon. Idrissa Maidaji ba haka dokar ke nufi.

Wadannan kalaman dai ba su hana ‘yan hamayyar fara jan damara domin kalubalantar wannan dokar da gwamnatin ta Nijar ke yi wa kallon dokar saka tsari a sha’anin sadarwar ba.

A jiya Talata ne ya kamata majalisar dokokin kasa ta tafka mahawara akan wannan sabuwar dokar sai dai saboda wasu dalilai aka dage zaman zuwa wata ranar da ba a bayyana ba tukun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG